Jummaʼa 9 Oktoba 2026 - 19:09
Ra’ayi: Operation ɗin “Guguwar Al-Aƙsa”; Tasiri da Sakamakonsa

Hauza/ Duk da ɗimbin asarar rayuka da dukiyoyi da aka yi, operation din “Guguwar Al-Aƙsa” ya zama wani muhimmin sauyi a tarihin gwagwarmayar al’ummar Falasɗinu. Wannan aiki bai dawo da batun Falasɗinu daga gefe zuwa tsakiyar siyasar duniya kawai ba, har ma ya bayyana ainihin yanayin gwamnatin Sahayoniya ga ra’ayin jama’ar duniya, tare da haifar da gagarumin ƙin jinin wannan gwamnati da kuma buƙatun ɗaukar matakan shari’a a matakin ƙasa da ƙasa a kanta.

Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito cewa, operation din “Guguwar Al-Aƙsa”, wanda aka fara a ranar 7 ga Oktoba, 2023, duk da cewa ya faru ne a wani yanki mai iyaka, amma tasirinsa da sakamakonsa sun bazu cikin sauri zuwa matakin duniya. Wannan aiki ya zama wani muhimmin sauyi a tarihin gwagwarmayar al’ummar Falasɗinu da ake zalunta, wadda ta shafe shekaru saba’in tana gudana.

Sauyin Ma’aunin Ƙarfi a Fa’idar Ƙungiyoyin Gwagwarmaya

Duk da cewa wannan aiki ya haifar da asarar dukiyoyi masu yawa, shahadar dubban mutanen Gaza, musamman mata da yara marasa laifi, da kuma shahadar shugabannin ƙungiyoyin Gwagwarmaya, tare da kisan kiyashin da gwamnatin Sahayoniya ta aikata cikin mugunta, amma ya sauya ma’aunin ƙarfi a matakin duniya zuwa fa’idar Ƙungiyoyin Gwagwarmaya a mafi yawan fagen yaƙi.

Dawo da Batun Falasɗinu Cikin Hankalin Duniya

Operation din Guguwar Al-Aƙsa ya faru ne a wani lokaci mai muhimmanci, lokacin da wasu sarakuna da shugabannin ƙasashen Larabawa suke ƙoƙarin daidaita hulɗa da gwamnatin Sahayoniya, yayin da ƙasashen mulkin mallaka suke son wanke sunan Isra’ila daga zargi da laifuffuka.

Sai dai wannan aiki ya dakile yunƙurin kyautata sunan Isra’ila da daidaita hulɗa da ita, tare da dawo da batun Falasɗinu da laifuffukan Isra’ila zuwa tsakiyar hankalin duniya.

Bisa rahotannin ƙasa da ƙasa, yarjejeniyar zaman lafiya ta Ibrahim, wadda tun farko ake da shakku a kanta, yanzu tana fuskantar jinkiri fiye da da. Ƙasashen Larabawa da dama ba sa ɗaukar daidaita hulɗa da Isra’ila a matsayin babban fifikonsu. Haka kuma, Pakistan ta bayyana a fili cewa shiga wannan yarjejeniya ya saɓa wa muhimman ƙa’idojin manufofin siyasarta.

Bayyana Ainihin Yanayin Gwamnatin Sahayoniya

Wannan aiki ya taimaka wajen bayyana ainihin fuskar gwamnatin Sahayoniya a idon al’ummomin duniya da ra’ayin jama’a. Sakamakon haka, ƙasashe da dama sun yanke hulɗarsu da Isra’ila. Haka kuma, an yanke hukuncin shari’a da dama dangane da laifuffukan da wannan gwamnati ta aikata, waɗanda ba a taɓa ganin irinsu a baya ba.

A watan Satumba na shekarar 2026, ƙungiyoyi kusan 200 daga ƙasashe 60 na duniya sun yi kira da a gurfanar da Isra’ila gaban shari’a bisa laifuffukan yaƙi da laifuffukan cin zarafin bil’adama. Sun kuma yi kira da a dakatar da aika mata da makamai.

Haka kuma, a watan Janairu na shekarar 2024, Kotun Ƙasa da Ƙasa ta Shari’a (ICJ) ta fitar da umarnin wucin gadi na ɗauri kan Isra’ila, amma wannan gwamnati ta ƙi aiwatar da su.

Ƙarfafa Kungiyoyin Gwagwarmaya a Dukkan Fagage

A tsawon shekarun gwagwarmaya tsakanin Falasɗinawa da gwamnatin mamayar Kudus, mayaƙan Falasɗinu sun kasance suna fuskantar gwamnatin Sahayoniya daban-daban. Amma bayan fara operation din Guguwar Al-Aƙsa, dukkan Ƙungiyoyin Gwagwarmaya da sauran ɓangarorin wannan ƙungiya, musamman ƙungiyar Hizbullah ta Lebanon, sun shiga fagen gwagwarmaya, inda aka samar da wani ƙawance mai tsarki na yaƙi da gwamnatin Sahayoniya.

Wannan haɗin kai da haɗin gwiwar mayaƙa a fagen yaƙi sun hana Isra’ila cimma mugayen manufofinta, tare da ƙara ƙarfafa kungiyoyin Gwagwarmaya.

Kamfanin Dillancin Labaran IRNA na Iran ya bayyana Guguwar Al-Aƙsa a cikin wani nazari a matsayin “girgizar ƙasa ta siyasa, soja da tsaro” ga Isra’ila, wadda ta bayyana raunin da ke cikin tsarin wannan gwamnati.

Rushewar Ƙaryar Ikirarin Ƙarfin Isra’ila

Bayan shekaru masu yawa tana samun cikakken goyon bayan ƙasashen Yamma, musamman Amurka, gwamnatin Sahayoniya ta kasance tana ikirarin cewa ba za a iya kayar da ita ba, tana kuma nuna tsarin kariyarta na “Iron Dome” ga duniya.

Sai dai Guguwar Al-Aƙsa ya bayyana a fili cewa wannan runduna ba ta da ƙarfin da take ikirari, kuma tsarin tsaronta yana da rauni sosai.

Masu nazarin harkokin ƙasa da ƙasa sun bayyana cewa tsarin tunanin tsaron Isra’ila ya fuskanci babban koma-baya bayan 7 ga Oktoba, kuma wannan gwamnati ta tsinci kanta cikin wani yanayi na yaƙe-yaƙe da fafatawa a yankin da suke ci gaba da raunana ta.

Mark Lynch, farfesa a fannin hulɗar ƙasa da ƙasa a Jami’ar George Washington, ya rubuta a cikin wani nazari da aka wallafa a mujallar Foreign Policy cewa dabarun Isra’ila bayan 7 ga Oktoba ba su samar da tsaro mai ɗorewa ba, a maimakon haka sun jefa ta cikin wani yanayi na gajiyar yaƙi da ci gaba da fafatawa.

Ƙaruwar Ƙin Jini da Ƙyama ga Isra’ila a Duniya

Guguwar Al-Aƙsa ta ƙara tsananta ƙin jinin duniya game da laifuffukan gwamnatin Sahayoniya. An gudanar da zanga-zanga masu yawa a ƙasashe daban-daban domin nuna adawa da mamayar Isra’ila da kuma goyon bayan al’ummar Falasɗinu. Wannan sauyi a ra’ayin jama’ar duniya ya kasance wani lamari mai muhimmanci wanda ba a taɓa ganin irinsa ba.

Bisa rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Saba na Yemen, ɗaya daga cikin fitattun sauye-sauyen siyasa da hulɗar ƙasa da ƙasa da wannan lamari ya haifar shi ne “keɓance gwamnatin Sahayoniya a matakin duniya”.

Wannan ya bayyana ta yadda matsayi da hoton wannan gwamnati suka ragu sosai a cibiyoyin ƙasa da ƙasa, jami’o’i da ƙungiyoyin ƙasashen Yamma, har ta kai ga ana kallonta a matsayin “gwamnatin da duniya ta fi ƙi”.

Sakamakon Shari’a da Hulɗar Ƙasa da Ƙasa

A fannin dokokin ƙasa da ƙasa, ƙarar da Afirka ta Kudu ta shigar kan Isra’ila bisa zargin kisan kiyashi a Kotun Ƙasa da Ƙasa ta Shari’a ta zama ɗaya daga cikin manyan shari’o’in da ake mai da hankali a kansu.

A watan Agusta na shekarar 2026, Afirka ta Kudu ta gabatar da hujjoji da ke nuna cewa Isra’ila ba ta bi umarnin kotun ba.

Haka kuma, ƙungiyar Hague (The Hague Group), wadda aka kafa a watan Janairu na shekarar 2025, ta karɓi baƙuncin ƙasashe 40 a watan Maris na shekarar 2026. Waɗannan ƙasashe sun taru ne domin nazarin matakan aikace-aikace da za a ɗauka wajen aiwatar da dokokin ƙasa da ƙasa a Falasɗinu.

Kammalawa

A ƙarshe, za a iya cewa Guguwar Al-Aƙsa, duk da dimbin asarar rayuka da dukiyoyi da ta haifar, ta zama wani muhimmin sauyi a tarihin gwagwarmayar Falasɗinu. Wannan aiki bai dawo da batun Falasɗinu daga gefe zuwa tsakiyar siyasar duniya kawai ba, har ma ya bayyana ainihin yanayin gwamnatin Sahayoniya ga ra’ayin jama’ar duniya, tare da haifar da gagarumin ƙin jini da buƙatun ɗaukar matakan shari’a a matakin ƙasa da ƙasa a kanta.

Duk da cewa Isra’ila tana ci gaba da aikata laifuffukanta tare da cikakken goyon bayan ƙasashen Yamma, rushewar ƙaryar ikirarin ƙarfin wannan gwamnati da samuwar haɗin kan Ƙungiyoyin Gwagwarmaya suna nuna babban sauyi a ma’aunin siyasa da ƙarfi a yankin da ma duniya baki ɗaya, wanda yake ƙara ba da muhimmanci ga manufar Falasɗinu.

Masu nazari sun yi imanin cewa tasirin wannan lamari na tarihi zai ci gaba har tsawon shekaru da dama, kuma zai sake fasalta alkiblar sauye-sauyen siyasa a yankin.

Marubuci: Sajjad Salimi

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha